Ingancaccan hadin karin Ni’ima na Matan aure har ma Budurwa

Ingancaccan hadin karin Ni’ima na Matan aure har ma Budurwa


 Kamar yadda a kulluma wasu Matan ke ta famar cewa suna da karancin Ni’ima, basa samin biyan bukata idan suna tarayya da Mazajen su wanda yana matukar ci musu tuwo a kwarya.

Zaka ga suna ta neman yadda zasu rabu da wannan matsalar amma abin ya gagara, wanda kuma ba karamin bacin abin yake jawo musu ba.

Domin idan aka ce Mace bata da Ni’ima to tamkar ta rasa wani arziki ne na jikin ta, domin Ni’ima tana daya daga cikin abin da Mace take alfahari da ita.

To a yau dai mun zo muku da wani hadi wanda zai karawa Mace Ni’ima, kuma ko bata da ita insha Allahu zata wadata da Ni’imar dai-dai gwargwado.

(1) – Hadin Kaza: Wannan wani hadine na mussaman wanda zai karawa Mace Ni’ima kuma zai zauna a cikin jikinta har tsawon wata uku 3 zuwa shida 6 ba tare data yi amfani da kayan da’a ba ko na bature.

Yadda za’a hada wannan maganin Ni’ina shine:

Za’a sami Kaza wadda bata fara kwai ba sai Ridi da Nonon rakuma, idan kin samo wadannan abubuwan ga yadda zaki musu.

Zaki yanka Kazar ki zare hanjin ba tare da anyi mata dunduwa-gunduwa ba, sai a zare hanjinta cikin zumbutunta zaki gyara Ridi ki shanya ya bushe sai ki daka shi.

Kina iya fara tafasa kazar, sannan ki zuba Ridin ki cikin zumbutun kazar sai ki zuba Nonon Rakuma ki daure zunbutun ki hada kayan miya kadan, sai ki zubo Nonon Rakumar a ciki, ki cigaba da dafawa har sai ya dahu sannan kici.

Wannan hadin Kazar da Ridi da Nonon Rakuma ba karamin karawa Mace Ni’ima yake ba, sabida da haka sai ku jarraba.

Hadin Kaza kashi na 2: Ana so ayima Budurwa ko Amarya da bata rage saura sati daya ba a daura mata aure domin yana kara gigita a Angonta.

AnA so lokacin da aka sanyawa Budurwa ranar aure, idan ya rage saura wata daya ayi bikin, a hada mata Kaza da Nonon Rakumi bayan taci wannan sai a rinka bata Gyada da Kwakwa da aya ta ringa ci, wannan hadin kuma ana so a yi shi ne ranar daren da Ango zai shigo daki da daddare.

• Kankana.

• Tuffa.

• Ayaba manya guda uku.

• Zuma Madara ta ruwa.

Wadannan abubuwan da muka lissafa muku suma idan Mace tana yawan amfani dasu, suna taimakawa wajan motsawa Mace Ni’imarta.

1- Garin alkama.

2- Garin sha’ir.

3- Garin farar shinkafa.

4- Garin nikaken dabino.

5-Nonon akuya.

Wannan kaya ana hadasu tare da Nonon Akuya suyi kwana uku sai a dafa a hada su da Nonon akuya adinga sha.

Post a Comment

0 Comments