Wasu Abubuwan Da Suka Faru A Kafafen Sadarwa 2022

Wasu Abubuwan Da Suka Faru A Kafafen Sadarwa 2022


 Wasu Abubuwan Da Suka Faru A Kafafen Sadarwa 2022


1. Kisan Haneefa Abubakar Da Safina

Hanifa Abubakar Yarinya ce ‘yar shekara 5 da haihuwa, wacce Mallamin makarantan su yayi garkuwa da ita daga karshe suka kashe ta.

2. Besty

Besty kalma ce da samari ke zargin ‘yan matan su na kiran wani wanda suke fifita shi fiye dasu.

3. Comrade/Kwamaret

Biyo bayan yajin aikin da kungiyar mallaman jami’o’i ASUU ta shiga, wannan yasa kafafen sadarwa sukayiwa matasa marasa sana’a chaaa! Wanda yakai ga ana yimusu isgili da kiran su Kwamarasawa.

4. Deligate

Ba shakka da ance daligate, mai karatu zai tuna lokacin zabukan fiddan gwanin zaben 2023, yadda masu zaben wato daligate suka cika aljihun su da kudaden ‘yan takara.

5. Yajin Aikin Kungiyar ASUU

Yajin aikin da kungiyar Mallaman jami’o’i sukayi na wata 9 yazama wani kanun labarai a kullum a kafafen sadarwa.

6. Kisan Deborah

Deborah Samuel dalibar kwalejin ilimi na Shehu Shagari dake Sokoto, wacce dalibai suka kashe bayan tayi kallaman batanci ga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wassalam)

7. Late Comer

Kalmar Late comer na nufin wanda yake zuwa a lokaci ‘kankani ya doke abokan takarar sa wajen budurwa a daura aure dashi wanda shi daga baya yazo.

8. Shigan Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo Masallaci Da Takalmi.

9. Safara’u

Tsohuwar jarumar shirin ‘kwana casa’in’ na tashar ‘Arewa24’ Safara’u wacce ta sauya sunan ta zuwa ‘Safaa’ a yanzun bayan komawar ta wakar gambara, sanin kowa ne tana daya daga cikin sunan dake zagaye a kafafen sadarwa.

10. Wakar Warr Da Chass

Wakokin mawaki Ado Gwanja da sukayi fice na Warr da Chass.

11. Pi Network

Manhajar mining ta Pi network wanda samari ke jiran fashewar sa su kudance, sai dai haryanzun bat fashe ba.

12. Mutuwar Queen Elizabeth

Mutuwar Sarauniya Ingila Elizabeth ll.

13. Fashin Jirgin kasan Abuja/Kaduna

Haren da ‘yan ta’adda suka kaiwa jirgin kasan Abuja-Kaduna a ranar 28 ga watan Maris, 2022.

Post a Comment

0 Comments