Tofa! Bayyanar Sabon Shirin Musa Mai Sana’a Me Suna “Tarkon Alkali” Yabar baya da Kura a Kannywood.

Tofa! Bayyanar Sabon Shirin Musa Mai Sana’a Me Suna “Tarkon Alkali” Yabar baya da Kura a Kannywood.


 Fitaccen Jarumin barkwanci a Masana’antar shirya Finafinan Hausa Musa mai sana’a Ya sako fastar wani sabon shirin sa me dogon zango Wanda yanzu haka an kan aikinsa ne amma hakan Yabar baya da kura inda mutane da dama keta tofa albarkacin bakinsu.

Wannan dai ya kasance daya daga cikin shirye shirye masu dogon zango Wanda ya fita daban da sauran domin an hango hotunan wasu yan mata babu riga atare dasu sai dai daurin gaba wanda hakan yabar baya da kura yasa mutane suna Zagi da Tsinuwa kan cewa wannan shirin sam bai dace ba.

Kamar dai yadda aka sani tuni dai aketa kalubalentar Masana’antar Kannywood akan irin yadda wasu Finafinan su da harkokinsu suke lalata Tarbiyyar al’umma amma har yanzu dai basu amince da hakan ba.

Sai gashi yanzu musa mai sana’a zai fitar da wani sabon shiri me suna Tarkon Alkali duk da cewa Matan da aka gani a hoto a iya cewa ba musulmai bane amma dai fim ne na Al’adar malam bahaushe wanda hakan ya saba ka’ida

To jama’a zamuso mukarɓi ra’ayoyin akan wannan saban shirin don jin tabakinku zamuso kubiyomu kaitsaye tasahinmu na tsokaci kaitsaye

Post a Comment

0 Comments