Amfanin Man Ridi Ajikin Dan Adam

Amfanin Man Ridi Ajikin Dan Adam


 Yadda za ayi amfani da man Ridi wajen magance cututtuka goma(10)

Man Ridi yana daya daga cikin iri-irin Man da aka sani, an dai dade ana amfani da man ridi wajen yin magungunan gargajiya, bincike ya nuna ana amafani da man ridi tun wajen shekaru dubu da suka wuce domin kariya daga cututtuka da suka shafi abubuwan da kan iya kawo cutar fatar jiki ko kuma cutauttuka da suka yi karfi kamar su ciwon suga, hawan jini da sauransu.

A wani Bincike da aka yi a makarantar Maharishi International College Fairfield Lowa a kasar Amurika an gano cewa dalibai na yin amfani da man ridi wajen wanke baki domin ba su kariya ta musamman wajen kare cutar dake fito wa a dasashin mutum wanda kansa gurin ya yi ta zafi har ya janyo asarar hakora.

Amfanin man ridi bai tsaya a nan ba domin ana amfani da shi wajen wanke kai don kashe kwarkwata ko amosanin kai. Ana kuma shafawa yara man ridi a jikisu don gyaran fatar jiki.

Wasu Cututtuka Da Man Ridi Ke Warkarwa cikin yaddar Allah

– Gyara fata da inganta lafiyar ta.

– Kara tsawon gashi da launin bakinsa.

– Kariya daga ciwon-daji.

– Gyara fatar jarirai da sanya su natsuwa a bacci.

– Hana rubewar hakori, kogon hakori da sauransu.

– Kariya daga ciwon asma da cututtukan numfasa.

– Rage hawan jini.

– Rage yawan sinadarin “Cholesterol”.

– Kariya daga ciwon suga.

– Inganta lafiyar kwakwalwa da sauransu.

-Domin samun lafiyayyar fata kuma, ana hada Man Zaitun da Man Ridi a mayar da shi abin shafawa a wata daya fatar jikin mutum za ta yi kyau kuma ta samu kariya daga cututtukan fata.

 

-Ciwon mara, ana shan cokali 2 safe da rana da kuma dare dan maganin ciwon mara.

– Ciwon cikin da baya jin magani da kuraje musamman na kazwa, a samu sabulun Zaitun a rika wanka da ita idan aka bushe sai a shafa man ridi a kalla a yi haka sau 2 a rana tsawon sati daya.

– Ciwon sikila, ana hada man ridi da Zuma a rika bawa mai matsalar yana shan cokali biyu safe da rana da dare har tsawon wata 2.

-Basir mai tsiro, a samu sassaken bagaruwa da ‘ya’yan ta a tafasa da ruwa idan suka tafasa in sun rage zafi sai a zauna cikin ruwan tsawon minti 15, idan aka fita a shafa man ridi a yi haka sau 2 ko wace rana tsawon kwana 10.

-Ashma, a rika shan cokali 2 safe da rana tsawon sati 3.

-Ulcer, a samu man ridi a hada da madara a rika sha da safe kafin a ci komai haka da dare bayan an ci komai sai a sha awa daya kafin a kwanta.

-Kumburin Jiki, ana shafa man ridi duk bayan an yi wanka da kuma in za a kwanta bacci.

–Soshe-soshe saboda yawaitar majina ko mataccen jin, sai a saka cokali 2 duk lokacin da za a ci abinci sannan kuma a shafe jiki da shi amma wajen shafawar dole sai an hada da man Zaitun.

-Ciwon mara lokacin fara al’ada, ana hada cokali daya na garin ridi da cokali daya na man Ridi da madarar gari a sha sau 3 kullum In sha Allahu za a samu sauki.

-Wanda yake da hawan jini ko matccen jini da sauransu sai ya rinka amfani da man ridi safe da yamma.

– Ri-ga-kafin hawan jini da shan inna, wanda ya dauki man ridi a matsayin abokin rayuwarsa wato kullum zai yi amfani dashi koda cokali daya ne zai samu kariya daga wadannan cututtuka kuma koda wace irin matsala ya samu kansa ciki.

Post a Comment

0 Comments