Ina masu tamaa da matsalar saurin kawowa a yayin jima’i da matan su to ga magani

Ina masu tamaa da matsalar saurin kawowa a yayin jima’i da matan su to ga magani


 Maigida bai kamata kafara tunanin biyan bukatarka ba kafin ta iyalinka, kasani wannan iyalinka ce biya mata bukata wajibi ne a kanka, ba wace ka daukoce domin zina ba, Wannan tunanin zaisa nan da nan kayi saurin kawowa kafin ita.

Galibi wannan tafi faruwa ga auren fari wajen maza tare da rashin samun wannan ilimin, to wannan damuwar takan taru a zuciyar matarka har ya zamana bata iya kawowa, sai tayi ta haihuwa ba
tare da jin dadin saduwar ba.

Hakanan dadewa ba’a sadu ba yakan janyo wannan matsalar ta saurin kawowa.

Hanyoyin magance wannan babbar matsala su ne kamar haka:

(1) Kayi kokarin shafa gabanka in kaji zaka kawo sai ka bari, ka sakeyi har kamar sau uku a kwana uku cikin mako guda.

(2) Kanemi tsawaita lokacin kawowar in kaji kafara sama sai kazare sai hankalinka ya kwanta saika mayar, wannan yana da kyau sosai.

(3) Idan sha’awarka ta fara sama sai kazaro ka wanke da ruwan sanyi kashare da tsumman da ya sha ruwan sanyi, sannan ka mayar, amma ruwan ba mai sanyin kankara ba domin yakan cutar da mutum.

(4) Idan iyalinka ce a kasa tabbas akwai saurin kawowa da wuri saboda saurin zuwan jini gabanka, amma in itace a sama bazaka sami wannan karfin ba, amma shima da ‘yar matsala kamar yadda Ibn Qayyim ya fadi).

(5) Amfani da condom albashi a dan huda gaban yadda ruwanka zai fita, kana iya hada biyu in har kana jin susarta.

(6) Idan sha’awarka tafara motsawa saika zarota, matarka tadora babban yatsarta a bisa kan tabaryarka manuniyarta a qasa saita matse da dan karfi ta ci gaba da matsewa, zaka danji zafi, nan take sha’awar za ta kintse, dan anjima kadan saika mayar, to amma fa kasani duk bayanan kar kabari sai sha’awarka tagama haduwa.

Awannan lokacin ba wani abu da zai iya taimakonka, wadannan hanyoyi sukan taimaka da kashi 95/100, sai yin amfani da maganin dagawar sha’awa wato (Prozac) likitoci sun sanshi, amma magungunan da ake yawan sayarwar nan gaskiya suna rage jin dadi.

Idan kai mai saurin kawowa ne, kuma daka kawo gabanka zai kwanta (sabo da irinka kenan), to kada kasauka, kaci gaba da qoqari, wannan yauqin ba zai jima ba zai daskare, hakan zai taimake ka kasake mikewa ko kuwa ita uwargidan ta sami
abin da take bukata.

Post a Comment

0 Comments