Abba ga Masoyansa: Ku yi min addu’a maimakon tattaki kan nasarar zaɓe da na samu

Abba ga Masoyansa: Ku yi min addu’a maimakon tattaki kan nasarar zaɓe da na samu


 Abba ga Masoyansa: Ku yi min addu’a maimakon tattaki kan nasarar zaɓe da na samu

Zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci magoya bayansa da ‘ya’yan jam’iyyar NNPP, da su tashi tsaye wajen yin addu’o’in neman hazaka da kuma jagora wajen ganin ya samar da ribar dimokuradiyya a jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa a Kano a yau Laraba daga Sanusi Dawakin-Tofa, kakakin kwamitin yakin neman zaben NNPP.

Addu’o’in, inji Yusuf sun wadatar a matsayin nuna goyon baya da kuma murnar nasarar da ya samu a zaben ranar Asabar maimakon tattaki na tsawon kilomitoci da wasu masoyansa ke shirin fara wa ba, musamman ganin halin da ake ciki na rashin tsaro da ‘yan fashi da garkuwa da mutane da ta’addanci kan zirga-zirgar mutane da kayayyaki a fadin kasar nan.

Yusuf ya kuma yi alkawarin inganta ayyukan more rayuwa da kyautata jin dadin tsofaffi da ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu da sauran su a jihar.

“Gwamnatin jihar Kano mai jiran gado za ta himmatu wajen samar wa al’umma gaɓa ta fuskar tsaro, lafiya, ilimi, tattalin arziki, samar da ababen more rayuwa da kyautata jin dadin tsofaffi, ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu da dai sauransu,” inji shi.

Mista Yusuf ya ce dole ne kowa ya tashi tsaye wajen ganin an tabbatar da ganin tafiyar Kwankwasiyya da kuma manufofin NNPP na samar da kyakkyawan shugabanci ga kowa da kowa a jihar.

Post a Comment

0 Comments