Gwamnatin Kano Ta Cire Dokar Hana Fita Da Ta Kakabawa Al’ummar Jihar

Gwamnatin Kano Ta Cire Dokar Hana Fita Da Ta Kakabawa Al’ummar Jihar


 Gwamnatin jihar Kano ta cire dokar hana fita da kakaba a jihar domin dakile duk wata tarzomar bayan bayyana sakamakon zabe da ta yi zargin ka iya afkuwa.

Kwamishinan yada labarai da kula da harkokin cikin gida na jihar, Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar. Ganduje Ya Sanya Dokar Hana Fita Bayan Sanar Da Nasarar Lashe Zaben Abba Gida-Gida

Sanarwar wacce kwamishinan ya fitar a daren jiya Litinin ta ce, gwamnatin ta dauki wannan matakin ne bayan ta sake yin nazari kan dokar da kuma yadda aka samu kwanciyar hankali a jihar.

Sanarwar ta yi kira ga Bankuna da al’ummar Jihar da su cigaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum, gwamnatin ta godewa al’ummar jihar bisa hadin kan da suka bayar a lokacin zartar da dokar zaman gidan.

A wani bangare kuwa, rundunar ‘yansandan jihar, ta baiwa al’ummar jihar tabbacin ba su kariya, inda kuma ta gargadi masu yunkurin tayar da rikici da su kuka da kansu, inda ta kara da cewa, ta tura jami’anta don cigaba da tabbatar da doka da oda a daukacin fadin jihar.

Post a Comment

0 Comments