Jihohin da za a iya samun matsala a sakamakon zaɓen gwamnoni – CDD

Jihohin da za a iya samun matsala a sakamakon zaɓen gwamnoni – CDD


 Wani rahoto ya ce taɓarɓarewar tsaro a sassa da dama, da yiwuwar hargitsa zaɓe, na iya zama illolin da za su shafi sahihancin zaɓen gwamnoni, da kuma yiwuwar samun sakamakon da bai kammala ba, ranar Asabar a Nijeriya.

Hakan a cewar rahoton na Cibiyar Bunƙasa Dimokraɗiyya da Raya Ƙasa (CDD), na iya yin tasiri ga niyyar ‘yan ƙasar na fita su yi zaɓe, baya ga ƙarancin man fetur da takardun naira da ake ci gaba da fama da su.

Duk da yadda sakamako ya kaya, rahoton ya ce za a zaɓi sabbin gwamnoni a jiha 17, sai jiha 11 inda gwamnoni masu ci ke neman wa’adi na biyu.

Ban da zaɓukan gwamnoni guda 28, za kuma a yi zaɓen ‘yan majalisun dokokin jihohi a duk faɗin Nijeriya.

CDD ta ce sahihan zaɓuka, muhimmin abu ne, amma zaɓen na ranar Asabar, 18 ga watan Maris, zai gamu da ƙalubale kamar na barazanar tayar da rikici da cikas wajen kai kaya da ma’aikatan zaɓe, saboda matsalolin tsaro da ƙarancin takardun kuɗi da na man fetur, akwai kuma raguwar amanna ga Hukumar zaɓe saboda rashin fara zaɓe kan lokaci da tangarɗar na’ura da suka baibaye zaɓukan shugaban ƙasa da na majalisar dokokin tarayya da ya gabata.

Rahoton dai na tsokaci ne kan wasu muhimman ginshiƙai guda shida waɗanda mai yiwuwa za su yi tasiri a zaɓukan gwamnonin jihohin.

Ginshiƙan, su ne:

  • Ƙabila ko tasirin addini
  • Ɗan takara ko jam’iyya?
  • Tsaro
  • Shirye-shiryen hukumomi
  • Rikicin cikin gida na jam’iyyu
  • Fitowar masu kaɗa ƙuri’a

Rahoton ya ce fushin da wasu ‘yan Nijeriya suka yi bayan zaɓukan watan jiya, na iya yin tasiri, amma isar kayan zaɓe a kan lokaci da inganta aikin na’urori da hanzarta ɗaukan mataki a kan jami’an zaɓen da aka samu da aikata ba daidai ba, zai magance raɗe-raɗin cewa INEC tana kwantar da kai ga buƙatun wasu gwamnatoci.

Ya ce zaɓen zai fi zafi a jihohi kamar Ribas da Lagos da Kano da Kaduna da Sokoto, haka ma Kuros Riba da Delta da Enugu da Zamfara ba ƙyallen yadawa ba ne, a daidai lokacin da ake iya samun mace ta farko a matsayin gwamna.

Rahoton ya kuma yi hasashen cewa yawan masu fita domin kaɗa ƙuri’a, na iya zarce kashi 29 cikin 100 adadin masu rijistar da suka yi zaɓen shugaban ƙasa da ya wuce.

Post a Comment

0 Comments