Mun ɗage zaɓen gwamna/ƴan majalisa ne sabo da mu saita na’urar BVAS

Mun ɗage zaɓen gwamna/ƴan majalisa ne sabo da mu saita na’urar BVAS


 Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta ɗage zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da za a yi ranar 11 ga watan Maris zuwa wata Asabar ɗin, 18 ga Maris.

Ɗage zaɓen ya biyo bayan gazawar hukumar na sake saita na’urar tantance masu kada kuri’a wato BVAS, don zaben jihar.

Kotun daukaka kara, a jiya Laraba ta baiwa INEC izinin sake fasalin BVAS din ta, domin zaben gwamnoni da na majalisun Jihohi da za a yi ranar Asabar.

Sai dai kuma INEC ɗin ta ce ba za ta samu damar kammala saita na’urar BVAS ɗin zuwa Asabar ba, shine ta ƙara mako daya domin ta samu damar saita na’urar.

Post a Comment

0 Comments