Rundunar ‘yan banga ta Najeriya reshen Nasarawa Eggon ta kai samame a maboyar masu garkuwa da mutane a Tudun Waya da ke karamar hukumar Nasarawa Eggon a jihar Nasarawa tare da cafke wasu mutane shida.
A yayin samamen, jami’an ‘yan banga sun kuma kubutar da wasu mutane bakwai da aka yi garkuwa da su a hannun wadanda ake zargin.
Kamar yadda shafin jaridar The Sun ya ruwaito, wadanda ake zargin suna da alhakin yawaitar garkuwa da mutane domin neman kudin fansa a kan hanyar Akwanga/Nasarawa Eggon/Lafia.
Bayan kama su, an kai wadanda ake zargin zuwa hedikwatar ‘yan sandan jihar da ke Lafiya domin ci gaba da bincike da gurfanar da su gaban kuliya.
Wannan nasarar da kungiyar ‘yan banga ta gudanar ya samu farin ciki daga mazauna yankin, wadanda suka shiga cikin fargaba sakamakon ayyukan masu garkuwa da mutane.
Bawa Ibrahim, daya daga cikin mazauna yankin, ya nuna jin dadinsa ga jami’an ‘yan banga bisa kokarinsu na tabbatar da zaman lafiya a yankin.
“Mun ji dadin ci gaban da aka samu a yau, domin ya zuwa yanzu ba
mu kwana da idanunmu biyu a rufe ba, amma na yi imanin cewa da kama wadannan ‘yan bindiga shida da ake zargi za mu fara samun zaman lafiya a yankin. Ya kara da cewa.
0 Comments