Saliyo Ta Fi Kowace Kasa a Africa Yawan Mata Da Aka Yi Musu Kaciya
Abin da aka mafi yawan lokaci yakan haddasa musu bala’i ne da yake da ƙungiyar al’ummar Bondo, wanda al’ada ne da aka kwashe shekaru da dama a na yi kuma ya kushi kade-kade da raye-raye inda ake shirya ‘yan mata su zama manyan mata. BBC ta tattauna da wani mutum da yake da yaƙinin cewa budurwarsa ta mutu ne sakamakon kaciyar da a ka yi mata.
Fatmata Turay na da shekara 19 da haihuwa a lokacin da mahaifiyarta ta bukace ta ta ziyarci ƙauyensu. An ƙaddamar da ita cikin ƙungiyar al’ummar Bondo. Bayan sa’o’i 36, Fatmata ta mutu.
Daga ranan 18 ga watan Agustan shekara ta 2016 da aka yi jana’izar ta, saurayin ta, kuma dan jarida Tyson Conteh y afara yin bidiyo. A wani bidiyo da ya yi daga baya, ya kalli kyamara ya yi bayanin abin da ya tunzura shi ya yi bayanin abubuwan da ke faruwa.
“Ina son in yi amfani da wannan fim din, wanda ke da muhimmanci a gare ni, in zakulo batun mahawara. Fatmata ba ta son ta ga wata yarinya ko mata ta sake mutuwa. Burin ta ke nan”
Ya ce Fatmata na masa magana a mafarki, kuma ta bukaci ya zakullo gaskiyan batun mutuwar ta kuma ya kawo karshen kaciyar mata. Kaciyar mata shi ne yanke wani bangaren al’uran mace ko kuma debe shi baki daya.
Hukumar kula da yawan jama’a na majalisar dinkin duniya ta ce kasashe 92 ke da wannan al’adar, amma an fi yin sa ne a yankunan Afrika da kuma gabas maso tsakiya. A kasashe kamar su Somalia, da Sudan da Djibouti akwai wani salon kaciyar da a ke yi mai suna “infibulation” inda a ke yanke lebban al’uauran mata sai a yi amfani da su wurin neman a shafe tsagun al’auran baki daya, sai da a bar wani dan bamgare don fitar fitsari da jinin al’ada. Idan mace ta yi aure, sai an sake yi ma ta
0 Comments