Gwamna El Rufa'i Ya Gargadi Masu Shirin Zanga Zanga A Kaduna

Gwamna El Rufa'i Ya Gargadi Masu Shirin Zanga Zanga A Kaduna


 Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa’I yaja kunnen masu yunkurin gudanar da zanga-zanga a sassan jihar.


Kwamishinan tsaron cikin gida Samuel Aruwan na kira ga jama’a da su kaucewa yada sakamakon karya a shafukan sada zumunta wanda zai iya haddasa tarnaki tun gabanin INEC ta sanar da na ta sakamakon.

A cewar Aruwan wajibi ne al’umma su yi dakon halastaccen sakamako daga INEC tare da gujewa yada jita-jitar da ka iya tayar da rikici.

Sanarwar gwamnatin ta Kaduna ta bukaci ‘yan takara su kaucewa zanga-zanga a gefen titunan lura da cewa sun yi tanadin ko ta kwana don kaucewa fuskantar makamantan rikicin.

Al’ummar Najeriya dai na ci gaba da dakon sakamakon zaben wanda yanzu haka hukumar INEC ke tattarawa ake kuma saran ta sanar da wanda ya lashe zaben kowanne lokaci daga yau litinin.

Post a Comment

0 Comments