Obasanjo Ya Bukaci Buhari Ya Soke Zaben Shugaban Kasa

Obasanjo Ya Bukaci Buhari Ya Soke Zaben Shugaban Kasa


 Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bukaci Buhari da ya soke zaben shugaban kasa da akayi ranar asabar na yankunan da aka samu tashin hankali. 

Obasanjo yace rahotanni sun nuna yadda aka samu matsaloli a wasu yankunan, kuma gabatar da sakamakon sun a iya haifar da tashin hankali. 

Obasanjo ya kuma zargi wasu jami’an hukumar zaben da tafka magudi wajen sauya alkaluman zaben da akayi kafin kai sakamakonsa inda aka tsara. 

Obasanjo ya shaidawa shugaba Muhammadu Buhari da a soke zaben domin sake gudanar da shi a ranar 4 ga watan gobe dan kaucewa jefa kasar cikin rikici. 

Tsohon shugaban na daya daga cikin wadanda suke goyan bayan takarar Peter Obi kamar yadda ya bayyana a watan Janairun da ya gabata. 

Post a Comment

0 Comments