ALAMOMIN NAMIJIN DARE DA MATAR DARE

ALAMOMIN NAMIJIN DARE DA MATAR DARE


 Daga cikin alamomin da mace zata gane tana da wannan matsalar sune:-

Shi wannan shaidanin zai dinga zuwa yana saduwa da ita acikin barci,yawancin mata suna tsintar kansu cikin wannan yanayi,amma sai su dauka halin mafarkine kawai,to a gaskiya ba haka lamarin yake ba.

Yadda lamarin yake shine:-


Duk mata ko budurwar da take irin wannan mafarkin zaka sameta tana fama da wadannan matsalolin zatace maka tana fama dasu.

Gasu kamar haka:-

1 Bacin rai ba tare da anyi mata komaiba,haka kawai taji tanajin haushin kowa har ma mijinta,ko kuma taji kamar mijin nata ya saketa,ita ta gaji da auren,wanda da zaka tambayeta laifin mijin nata bazata iya fadin komaiba akai,kai wata rana ma taji ta tsani y’ay’an data haifa.

 

2 Yawan ciwon kai daga lokacin zuwa lokaci kuma baya jin magani ko kadan.

 

3 Tsananin ciwon kirji da ciwon baya mai tsanani.

 

4 Tsananin ciwon mara lokacin jinin al,ada da kuma zubar wani ruwa daga farjin mace,kuma tasan wannan ruwan ba al,adarta bane,
kuma ya kasu kamar haka:-

 

  •  mai yauki 
  •  marar yauki
  •  ko mai kauri kamar koko tare da yawan kaikayi 
  • ko fesowar kuraje masu zafi.

 

5 Idan mijinta yana sauwa da ita sai take jin zafi,ko kuma yana saduwa da ita batajin zafi,amma bata samun biyan bukata.

 

6 Kusan sallar magriba sai ta fara jin zazzabi ko faduwar gaba ko yawa firgita,ko kasala da bacin rai.

 

7 Idan ta dauki al-qur’ani zata karanta,saita rinkajin kasala, da hamma mai sanya hawaye, kuma tanajin barci sosai,amma da zarar ta ajiye Al-qur,anin sai taji ta wartsake kamar ba itace takejin bacci dazu.

 

8 Kuma idan ta kwanta zatayi barci sai ta kasa yin baccin tayi ta juyi akan katifa,idan mijinta yazo kusa da ita sai take jin firgici da tsoro.

 

9 Ko ta wayi gari gashin kanta ya dinga zubewa ko ya canja ya zama jawur,lebenta kuma ya rinka bushewa ko yayi jawur.

 

10 Yawan kaikayin ido da kaikayin kai na amosani,amma ba amosani bane.

 

11 Yawan kaikayin kunne dana hanci kamar mura zata kamata,amma kuma ba mura bace,ko yawan kumburin ciki.

12 Yawan zubar da jini wanda ba jinin hailaba,ko hailarta ta dinga yi mata wasa.

 

Sannan kuma harma wacce bata da aure budurwa ko bazawara zata iya tsintar kanta acikin wannan matsalar,amma ita ban-bancinta da mai aure.


shine kamar haka:-

[1] Ita marar aure zata kasance duk lokacin da wani yazo wajenta da maganar aure kamar za,ayi sai abin ya lalace daga bangarenta ko bangaren wanda zai aureta.

 

[2] Zata dinga munanan mafarkai tare da ganinwani namiji yana zuwa yana saduwa da ita acikin bacci da fuskar wanda ta sani ko da fuskar yar,uwarta mace.

 

[3] Sannan zata rinka samun cututtuka masu wuyar waraka,kai harma da yawan zubar da jini ko jin ciwo,ko jinin yake zuba amma ba lokacin hailarta ba,ko ta rinka jin kasala ayayin da take karatun al-qur’ani tana fara karatun sai hamma ,kasala su baibayeta,ko kuma idan ana sallama da ita,sai ta rinka jin faduwar gaba ko tsorata.


4 Kuma zata yawaita samun sabani da kiyayya tsakaninta da iyayenta ko ‘yan uwanta ko jama’a ko kuma ta zama mai rashin kunya da rashin magana da iyaye da sauran dangi. Allah ya kara tsaremu daga sharrinsu tare da yi mana katangar karfe dasu, amin.
Zuwa Nan Gaba Insha Allahu Zamu Kawo Hanyoyinda Za’abi Dan Samun Waraka!

Post a Comment

0 Comments