Kar ka bari a ziga ka kai rigima da Kwankwaso, Sheikh Ibrahim Khalil ya shawarci Abba Gida-Gida

Kar ka bari a ziga ka kai rigima da Kwankwaso, Sheikh Ibrahim Khalil ya shawarci Abba Gida-Gida


 Sheikh Ibrahim Khalil, wanda ya yi takara a jam’iyyar ADC, ya shawarci zaÉ“aÉ“É“en gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da kada ya sake ya bari wasu gurbatattun Æ´an siyasa su ziga shi ya yi rigima da mai gidansa, Rabi’u Musa Kwankwaso.

Sheikh Khalil, wanda ya zo na huɗu a zaɓen gwamna da a ka yi ranar Asabar, ya bada wannan shawara ne a wani shiri a Freedom Radio a Kano a jiya Talata.

A cewar Sheikh Khalil, Abba Kabir Yusuf ya maida hankali wajen toshe duk wata kofa da za a a iya amfani da ita wajen haddasa rigima tsakanin sa da Kwankwaso.

Ya kara da cewa a matsayin sa na É—an sarauta, wanda kakanninsa suka yi shura wajen hakuri da dattaku, to ya daure ya gaji wannan halin ya yi hakuri da mai gidansa Kwankwaso da yan Kwankwasiyya.

Ya kuma shawarci Abba da ya sani cewa al’ummar Kano zai mulka ba Æ´an Kwankwasiyya ba, inda ya shawarci zaÉ“aÉ“É“en gwamnan da ya yi kokari sosai wajen cika alkawuran da ya É—auka wa mutane a jihar.

“Kada Abba ya bari a ziga shi ya yi rigima da Kwankwaso. A matsayin sa na É—an sarauta, wadanda aka sani da sun gaji hakuri, to ya daure ya yi hakuri tsakaninsa da mai gidansa da kuma yan Kwankwasiyya. Sannan ya toshe kunnen sa ga sauran al’ummar jihar tunda dama mulki ya gaji yabo da suka.

“Abu na biyu shine, Abba ya yi kokari ya zamana cewa gwamnatin sa gwamnati ce ta al’ummar jihar Kano ba gwamnatin Æ´an Kwankwasiyya ba,” in ji Sheikh Khalil.

Post a Comment

0 Comments