Malam Dan Allah kayi min cikakken bayani akan Jigida da amfanin ta, Nagode.

Malam Dan Allah kayi min cikakken bayani akan Jigida da amfanin ta, Nagode.


 Amsar tambayar wata Baiwar Allah (Da fatar Kin gani)


Gabatarwa:

Jigida, Ileke, Giri-giri ko Waist Beads abune da yake da daÉ—aÉ—É—en tarihi a Æ™asashen Afrika, wanda ake da amannar cewa ta samo asali ne daga matan Æ™asar Egypt, idan muka É—auki Afrika ta yamma, musamman Nigeria za muga cewa matan su suna amfani da Jigida tsawon zamani daga mabambantan Æ™abilun Æ™asar tun kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka. Duk da akwai waÉ—anda suke da ra’ayin cewa Matan Æ™abilar Yarbawa ne suka sanya Jigida ta zama sananniya a faÉ—in Nigeria. MawaÆ™a daban-daban a Nigeria sunyi mata waÆ™a kamar irin su: Mamar MawaÆ™a Maryam Fantimoti, dasu Mr. 442, Ola of Kano & Safa, inda suke cewa: “Wacce ba tasa Jigida, ai ko tana ruwa”

Saidai kamar yadda Google Arts & Culture ya bayyana shine, Larabawa da Portuguese sune suka fara shigo da Jigida a ƙasashen Afrika ta gabas domin Kasuwanci, tun daga ƙarni na 16 har zuwa na 18, kenan Jigida tazo ƙasashen Afrika ne kimanin Shekaru ɗari biyar baya (500 Years Back)

Yaya ake saka Jigidar ?

Akwai yanayi daban-daban da mata suke saka Jigida, ya danganta ne da ita Macen, amma dai wasu matan sukan ɗaura ta ne sannan su kawo zani ko Skirt su rufe ta, (Waɗanda suke sanya ta irin haka galibi ba zaka riƙa jin motsin ta ba idan suna tafiya ko wani abu) wasu matan kuma sai sun ɗaura Zanin ko Skirt sannan su kawo ta su ɗaura (Matan da suke sanya ta irin haka, to idan suna tafiya ko suna wani abun, zaka riƙa jin ƙarar ta) wasu kuma sukan sanya ta ne a saman kayan su, wato zasu fito da ita fili (Duk da dai Matan basu fiye yin haka ba sai wasu tsirarun ƙabilu) kazalika, wasu matan sukan sanya ta ne sannan su kawo Pant su saka a kanta (Wato Pant din zai rufe ta, amma mafi yawanci sai idan Jigidar mai round ɗaya ne) saboda Jigidar ta kasu kashi-kashi, akwai wacce za ku ganta Round ɗaya ne kawai, kuma Stones ɗinta ƙananu ne, so irin

wannan itane ake sakawa sannan a kawo Pant a rufe ta, akwai kuma wacce za ku ganta ta kai naÉ—i 5 har zuwa sama idan aka naÉ—e ta Æ™ugu, to irin wannan ba’a sanya Pant a rufe ta. Sannan wata za kuga tana da Manyan Stones wata kuma Æ™anana, ya danganta ne dai.

Nawa ake siyar da Ita ?

KuÉ—in ta ya danganta da yanayin ta da kuma kasancewar Round nawa ce, amma dai mafi yawan Lokaci kuÉ—in ta yana farawa ne daga ₦300 har zuwa sama.

To, Menene amfanin Saka Jigida a Wurin Mata ?

Kamar yadda muka sani, duk abinda kaga mutane sunayi to dole akwai dalilin yin sa (Ko dalilin ya zama karÉ“aÉ“É“e ko akasin haka) don haka ita ma Jigida akwai dalilan da ya sanya mata suke sanya ta, duk da yanzu tana shan suka a wurin wasu saboda yanzu mata (wasu) sun canja ta daga yadda akasan amfanin ta, sun mayar da abun magani. Idan kana zuwa Shagon da ake siyar da Maganin kayan Mata zaka riÆ™a ganin irin wannan Jigidar ta magani, a mafi yawan lokuta zaku ganta fara ce (duk da akwai different Colours, Amma dai fara tafi yawa) sannan za kuga tana yin haske idan dare yayi (amma akwai waÉ—anda suke yin hasken kuma ba na magani bane, don kar kaga matar ka da irin ta kace ta magani ne) Kazalika, a irin wannan Jigidar ta Maganin Kayan Mata, to su matan sun fi Son wacce akazo da ita daga Sokoto ko Zamfara, saboda sunyi amannar cewa Maganin kayan Matan da akazo dashi daga Zamfara ko Sokoto yafi kyau sosai, saboda haka irin wannan Jigidar kuÉ—in ta yana kaiwa: ₦3k, ₦4k har ₦5k ya dai danganta da wajen da zaki siya, to ita irin wannan Jigidar ta maganin Kayan Mata, Matan sunyi amannar cewa Indai mace ta sanya ta to zata Mallake Mijin ta, sannan zai riÆ™a jin daÉ—in ta once he has sexual Intercourse with her lokacin da Jigidar ke É—aure a Æ™ugunta.

Ga wasu daga cikin amfanin ta:

1• Tana sanya jikin Mace yayi Shape
2• Tana rage tumbi, ga matan da suke dashi
3• Tana Æ™ara girman Hips
4• Tana Æ™ara ma Namiji Kuzari
5• Tana sa Namiji ya riÆ™a jin Sha’awar Mace
6• Ana amfani da ita wajen gane Mace ta Æ™ara Æ™iba ko ta rage
7• Ana sanya ta Saboda Kwalliya
8• Ana sanya ta don nuna cewa yanzu yarinya ta zama Cikakkiyar Mace
9• Æ™asashen Zambia da Malawi suna sanya ta lokacin da suke da ciki
10• Tana nuna cewa yanzu mace ta isa a sadu da ita (A wasu Æ™asashen)
11• A wasu al’adun, Mace tana sanya ta ne don nuna cewa ba’a taÉ“a Saduwa da ita ba, Mijin ta ne kawai zai cire mata ita bayan sunyi aure
12• Tana burge (mafi yawan) Maza

Post a Comment

0 Comments