Sarkin Kano ya ɗaga likkafar wasu hakimai da sabbin naɗe-naɗe

Sarkin Kano ya ɗaga likkafar wasu hakimai da sabbin naɗe-naɗe


 Sarkin Kano ya ɗaga likkafar wasu hakimai da sabbin naɗe-naɗe

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya daga Darajar wasu Hakimansa da kuma nada wasu sababbi.

Wannan na kunshe a wata sanarwa da Abubakar Balarabe Kofar-Naisa,
Babban Sakataren Yada Labarai na Masarautar Kano ya fitar a yau Juma’a a Kano.

Ya ce daga cikin Hakiman da aka daga darajarsu sun haɗar da Sarkin Dawakin Tsakar Gida, Alhaji Ahmad Ado Bayero zuwa Dan Iyan Kano , sai kuma Turakin Kano, Alhaji Lamido Sunusi Bayero zuwa Sarkin Dawakin Tsakar Gida.

Sauran sun haɗa da Tafidan Kano Alhaji Mahmoud Ado bayero, wanda ya zama Turakin Kano, yayinda Dan Galadiman Kano Alhaji Haruna Rasheed Sunusi aka daga Darajarsa zuwa Tafidan Kano, sai Alhaji Kabiru Tijjani Hashim Dan Isan Kano ya zama Dan Galadiman Kano.

Sauran, a cewar sanarwar, su ne Dan Lawan din Kano Alhaji Bashir Ado Bayero ya koma Dan Isan Kano, Alhaji Yahaya Inuwa Abbas Dan Majen Kano ya zama Lawan din Kano.

Kazalika, in ji sanarwar, Mai Martaba Sakin ya nada Alhaji Ahmad Kabiru Bayero a Matsayin Barde Kerarriya da kuma Alhaji Abdulkadir Mahmoud a Matsayin Magajin Rafin Kano.

“Da ya ke Jawabi jin kadan da nadasu, Mai Martaba Sakin yace an basu wadannan Sarautu ne saboda cancantaru da kuma hidimtawa al’uma.

“Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukace su zamo jakadu nagari a duk inda suka sami kansu tareda ciyar da masarautar ta Kano gaba,” in ji sanarwar.

Post a Comment

0 Comments