Cin Zarafi Ta Fuskar Lalata Da Mata Ke Fuskanta A Kasar Kenya – Video

Cin Zarafi Ta Fuskar Lalata Da Mata Ke Fuskanta A Kasar Kenya – Video


Cin Zarafi Ta Fuskar Lalata Da Mata Ke Fuskanta A Kasar Kenya – Video

Majalisar Dokokin Kenya ta bayar da umarnin fara wani binciken gaggawa kan zargin cin zarafi ta hanyar lalata a wata gonar ganyen shayi, bayan rahoton BBC ya bankaɗo abin da ke gudana a wajen.

‘Yar majalisar ƙasar Beatrice Kemei ta ce ta kalli rahoton amma “cikin kaɗuwa”.

Rahoton na BBC ya gano cewa cikin shekaru sama da mata 70 da ke aiki a gonar ganyen shayin sun fuskanci cin zarafi ta fuskar lalata daga shugabanninsu na kamfanonin Birtaniya biyu, Unilever da James Finlay.

Kamfanonin sun ce sun girgiza da wannan zargin da ake musu. Lamarin da ya kai ga dakatar da wasu shugabanni hudu.

Gidauniyar Fairtrade ta bayyana wannan zargi a matsayin wani abin tashin hankali.

Ta kuma ce wannan bincike da BBC Africa Eye ya yi – ”ba wani abu ba ne illa ni ma hakan ya faru da ni a gonar ganyen shayi.”

Ms Kemei wadda ita ce ke wakiltar yankin da gonar take, Kericho, rahoton ya nuna wani ɗan abu ne da yake faruwa na cin zarafin mata a wannan gonar a ƙasar Kenya.

‘Yar majalisar Beatrice ta ce da mamaki a ce irin waɗannan lamura suna faruwa har yanzu.

“Yau wata rana ce mai wuya a wurina a matsayina na mace, shugaba, kuma ‘yar ƙasar Kenya.” in ji ta.

Ta kara da cewa : ”A yau an tunatar da ni cewa har yanzu ana ci gaba da bautar da mutane a wannan ƙasa tamu; Ba zan iya bayani ba kan yadda wani namiji ya rika cin zarafin mata a gonar ganyen shayi cikin sama da shekara 30 kuma babu wani abu da aka yi,” kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka ambatota nata fada.

Mataimakiyar shugaban Gladys Shollei ta bayar da umarnin kafa kwamitin majalisar da zai gudanar da bincike kan wannan zargin cikin mako biyu.

A binciken da BBC ta gabatar, wata mata ta ce ta kamu da ƙwayar cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV ta dalilin shugabanta da ke lura da ita a kamfanin, bayan matsa mata da ya yi sai ya kwanta da ita.

Wata kuma ta ce manajanta ya dakatar da ita daga aiki har sai ta amince ta kwanta da shi.

“Ba wani abu ba ne illa azabtarwa; idan yana son kwanciya da ke, za ki samu aikinki yadda kike so,” in ji ta.

An gayyaci ma’aikaciyar BBC da ta yi shigar-burtu a matsayin mai neman aiki, tattaunawa a kamfanin James Finlay & Co.

An tsara wannan jarrabawar neman aikin a wani ɗakin otal, inda wanda zai ba ta aikin ya ce ta zauna a jikin wata kofa ta kuma cire kayanta.

Mutumin wanda ke aiki a kamfanin Finlay sama da shekara 30, daman matan da BBC ta tattauna da su sun ce suna masa kallon wani babban maƙiyi, kasancewar shi ne wanda suka fi ambatar sunansa a zargin.

”Zan ba ki kuɗaɗe masu yawa, sannan zan ba ki aiki. Zan taimaka miki, ni ma ki taimaka min,” in ji shi.

“Mu kwanta sannan in mun gama. Ki zo ki kama aiki.”

Kamfanin Unilever ya fuskanci irin wannan zargin, sama da shekara 10 da suka gabata inda ya ƙaddamar da wani tsari na rashin amincewa da duk wani abu mai kama da cin zarafin ta hanyar lalata.

Bayan wannan akwai kuma wani tsari na kai ƙara domin ɗaukar mataki, sai dai BBC ta gano cewa akwai hujjoji da ke nuna idan aka kai ƙarar kan zargin cin zarafi babu matakin da ake ɗauka a kai.

Wakilin BBC Tom Odula ya tattauna da wasu mata da ke aiki a kamfanonin gonar ganyen shayin biyu.

Da dama sun shaida masa cewa saboda aiki ya yi ƙaranci, don haka ba su da wani zaɓi illa su bayar da kansu ta fuskar lalata domin samun abin da za su rayu da shi.

Babban kantin sayar da kaya na Birtaniya, Tesco, ya ce ya ɗauki wannan zargi da muhimmanci, kuma yana tattaunawa da kamfanin Finlay domin tabbatar da an ɗauki matakan da suka dace.

A wani martani ga binciken na BBC, kantin Sainsbury ya ce ba shi da alaƙa da wannan zargi da ake yi wa kamfanonin.

A ranar Litinin, ya fitar da wata sanarwa wadda ta ce “za a ɗauki matakin da ya dace domin tabbatar da aminci ga ma’aikata da suke aikin kawo ganyen shayi.”

A wata sanarwa da Starbucks ya fitar a ranar Litinin, ya ce ya yi matukar damuwa da wannan lamari kuma kai tsaye ya ɗauki matakin dakatar da sayayya daga James Finlay da ke Kenya.

Shi ma kamfanin Finlay ya ce ya dakatar da manajan da ake zargi kuma ya miƙa shi ga ‘yan sanda.

Yana gudanar da bincike kan “ko kamfanin da ke aiki a Kenya na da masaniya kan wannan cin zarafi” in ji kamfanin.

Unilever ya ce waɗannan zarge-zarge; “abin damuwa ne da tashin hankali.”

Kamfanin ya sayar da harkokinsa da yake yi a Kenya, yayin da BBC ke naɗar yadda aka yi cinikin a cikin sirri.

Sabon mai kamfanin Lipton da Infusions ya ce ya dakatar da manajoji biyu, ya kuma bayar da umarnin gudanar da bincike mai zaman kansa.

 KALLI BIDIYON ANAN


Post a Comment

0 Comments