YADDA AKEYIN KUNUN GORUBA DA YADDA ZAKU SARRAFA TA HANYOYI DADAMA DA KUMA AMFANINTA GA LAFIYARMU

YADDA AKEYIN KUNUN GORUBA DA YADDA ZAKU SARRAFA TA HANYOYI DADAMA DA KUMA AMFANINTA GA LAFIYARMU


 YADDA AKEYIN KUNUN GORIBA DA KUMA YADDA AKE SARRAFATA TA HANYOYI DADAMA DA AMFANINTA GA LAFIYARMU



KAYAN HADI:-

_Gero

_Naman goriba

_Citta

_Kanunfari

_Suger


Dafarko zaki surfa geronki ki shanyashi yabushe saiki feceshi kifitar da dusar,saiki wankeshi kisa citta da kanunfari kibayar amarkado miki,saiki taceshi da rariya irin yadda ake tace kunu,saiki dafa naman goriba kamar yadda ake dafa tsamiya,idan yatafasa saiki dibi kullin qasan mai dan kaurin kizuba a abinda zaki dama kunun saiki tace ruwan naman goribar da kika dafa akan kullin shine amadadin tsamiya sai ki bari yadansha iska sai saka gasarar kunun kijuya kisa suger.


 

(Amfaninsa ajikin mutum)

Yana rage kitsen dake cikin jini

Yana kariya wajen kamuwa da ciwon daji(ulcer)



AMFANIN GORIBA DA MAGUNGUNAN DA TAKEYI


 

Ganin cewa sannu a hankali mun fara mantawa da wasu tsirran itatuwan da muka taso muka tarar a cikin kasarmu wadanda Allah ya halitto muna dake da dimbin amfani ga jikin Dan-adam masu zama a matsayin magani na musamman ga wasu cutukka.Sai gaya muna juya baya ga wadannan tsirran itatuwan saboda rashin sanin dimbin alfanon dake tattare da su .inda muka fi baiwa maganin bature na Multivitamins muhimmanci.Anan ina nufin maganinda ke samarda wasu sinadirran gina jiki da karin kuzari sabili da wasu cutuka.Wanda nayi imani da za a nuna mana tsirran itatuwan da ake hada wadannan magunnan masu tsada na Multi vitamins,supllements,Blood tonic da dai sauransu da a hakika za mu tabbatar da cewa ashe mune da magani a cikin gida,amma saboda rashin sani sai gaya muna yasuwa muna fita har waje muna siyowa da kudinmu da kuma tsadar gaske.



Ganin haka yasa shafin ciwo da magani ya maida hankali dan bankado da amfanin wadannan tsirran itatuwan da muka fara mantawa dasu.


 

Ita dai goriba sananniyace a kasashe masu yawa na fadin duniya,tun daga Egypt,Sudan,Kenya,Tanzania,malasia,


Indonesia,Singapore,Viatenam,Pakistan,India,Thailand da sauransu.


A can baya da ganyentane ake saka tabarmin kaba da kuma littafan rubutu dukda yake ko a wannan lokacin ana cin diyan goriba saidai wasu na kallonta kamar kayan kwalama ne kawai irin na yara,inda wasu ke ganin ai sai mai karfin hakora yake iya tamna goriba.


Kimiyya tayi amanna cewa diyan goriba na kumshe da wasu muhimman nutrients da minerals da kuma proteins gami da fatty acids wadanda dukkaninsu suna matukar amfanar jiki dan inganta lafiyar jikin dan adam.



Akoi vitamins kamar haka a qumshe da diyan goriba -


Vitamin A.

Vitamin B.

Vitamin C.

,Zinc.

Iron.

fiber.

glucose.

Nitrogen.

fosfor.

da sinadiran linoleic acid

.saponins

coumarin.

hydroxycinnamates.

essential oils.

flavonoids. Da sauransu.

 


1.) Idan kana fama da poor digestion (ina nufin watakila kaci abinci amma sai ya wuni a cikinka yana wahalda kai ko ya ki narkewa a yanda ya dace ko ya janyo maka kabewar ciki ko taurin bayan gari(constipation) to sai a nemi garin diyan goriba a saka cokali daya babba a cikin rabin cup karami na ruwan zafi sai a sha,safe da yamma tsawon sati daya.


 

2.) Zafin jiki -Kodai a sabili da wani aikine mai janyo gajiya ko tafiya mai nisa ko wata damuwa haka(pressure) to sai a sha garin goriba.Amma kada a saka suga tana daukeda natural sugar da kanta.


 

3.) mai fama da yawan buguwar zuciya akai akai da dalili ko da rashin sanin dalili,sai a nemi garin goriba a tafasa cokali biyu manya sai a tarfa zuma cokali uku a sha.


4.) karfin kwakwalwa - a dama garin goriba a tareda ruwan kwakwa sai a tarfa zuma kadan a lashe da safe kandan aci komai.Sai a fake yin haka.


5.) Ciwon suga - mai fama da wannan matsalar ta ciwon suga zai kula da irin abincin da yake ci.


Saboda baya yiwuwa kana fama da suga a jiki amma kana cin abinci son ranka wanda hakan kan hana magani yin tasiri kuma yana kara ta'azzara zafin ciwo.za a nemi ganyen manguro sabon tofo dan yafi magani sai a wanke ganyen da kyau a tafasa cup daya na ganyen sai a tace ruwan a sanya cokali karami na garin goriba a tace da kyau sai a sha da safe bayan an karya sai a fake motsa jiki.za a yiwa Allah godiya.


Basir -musamman mai tsiro sai a fake amfani da garin goriba za a dafa a tace sai a tarfa garlic oil made in Egypt a sha.



Natural Antibiotic ne-waton yana warkarda cutukkan da kwayar cuta ta bacteria ke da alhakin haddsata,amma fa wannan hadin baya tasiri ga kwayar cuta ta virus ko fungi.waton akoi wasu enzymes a ciki wadanda ke kashin kwayar cuta ta bacteria.

Za a hada madara da garin goriba cokali daya sai a dama da kyau a sha.


Yawan damuwa(stress/anxiety) idan kana fama da yawan damuwa a sabili da wani abu da ya shafi rayuwa ko baka da natsuwa inda zaka kasa yin bacci.Sai dai wannan hadin yana bukatar cikakken bayani.


 

Yana sauwake fitar fitsari da kuma inganta lafiyar koda.Sai a rinka tafasawa ana sha.


Shawa ga mata - macen dake son ta ji kanta kamar budurwa waton kamar wacce take balaga to sai ta nemi garin goriba misalin gongoni daya na madara sai ta nemi garin dabino da kuma ruwan kwakwa amma fa kada a saka a fridge kuma kada a tafasa za muyi bayanin wannan nan zuwa gaba.


Karfin maza - sai a dake namijin goro a gauraya da garin goriba.


Kasala-A nemi garin goriba sai a tafasa a sha nan take idan anci abinci musamman da dare.


Karin ruwan maniyi - a nemi kwai guda biyu zuwa uku sai a nemi albasa qatuwa a yayyanka ta gunduwa gunduwa a marmasa garin goriba a soya qwan amma kada a bari kwan ya kone ayi shi jagab jagab haka sai a fake ci sau daya a kullum.


Karfin hakora -a zanka tamna goriba.


Ni'ima ga mata - A gauraya garin aya da garin goriba sai ayi gumba.


Karin lafiyar ga jiki -A dama kunun alkama sai a sanya garin goriba

Post a Comment

0 Comments